Ticker

6/recent/ticker-posts

MENENE CRYPTO CURRENCY

 CRYPTOCURRENCY




Menene Cryptocurrency?

Jama’a da yawa suna tambaya akan Kasuwancin Cryptocurrency da kuma yadda ake sarrafashi, kasancewar bai jima da shigowa wannan zamanin ba.


Cryptocurrency a taƙaice kasuwanci ne na canjin kuɗaɗe a yanar gizo ba tare da shigowar wata hukuma ko banki ba, wato canjin kuɗaɗe ne da ake yi kaitsaye tsakanin mai siyarwa da mai siya.


Misali yadda ake canja kuÉ—aÉ—en daga Dollar zuwa Naira ($ => ₦) ko zuwa kuÉ—aÉ—en wasu Æ™asashe daban, haka ake canja waÉ—annan kuÉ—aÉ—e na intanet zuwa wani kuÉ—i.


Saboda yawaitar hatsaniya da sauran dalilai, a yanzu ba a buƙatar sai mutum ya je banki kafin ya iya biyan kuɗi a yanar gizo ko ya tura zuwa wata ƙasa, cikin hanyoyin da ake bi na zamani akwai wannan hanyar wacce ta zama ruwan dare a wannan zamanin. Kuɗaɗen intanet za su ba wa mutum damar musayar kuɗaɗe a yanar gizo ba tare da shigowar wata hukuma cikin lamarin ba.


Rashin shigowar hukuma cikin lamarin ba shi ke nuna cewa ba ingantacce ba ne, haƙiƙa an jima ana wannan harkar kuma yawan damfara yana raguwa ta dalilinsa.


Cryptocurrency kaitsaye shine kuÉ—aÉ—en Intanet, haka zalika Cryptobusiness kuma shine kasuwancin kuÉ—aÉ—en a yanar gizo.


Yadda tsarin yake

Ana siyan waÉ—annan kuÉ—aÉ—e na intanet domin siyar da su ga wasu a duk lokacin da buÆ™atar hakan ta taso. Saboda yadda waÉ—annan kuÉ—aÉ—e suke tashi, misali yadda (Dollar, $) take tashi a yanzu, siyanta zai iya zama riba ga mutum – ta yadda za a siya a yau, kashegari kuma a siyar musamman idan ta Æ™ara kuÉ—i. Haka harkar kasuwancin cryptocurrency yake a yanar gizo.


Ire-iren Cryptocurrency

KuÉ—aÉ—en intanet na wannan harkar ta cryptobusiness suna da dama, a cikin mafiya shahara sun hada da:


Idan aka ɗauki Bitcoin musamman yadda yake tashe kullum a kasuwa, zai fi sauƙin harka sai dai yana da tsada. A yanzu haka Bitcoin 1 ya kai N14,670,562. Ana lissafinsa da 0.1 zuwa sama. Sannan ana buɗe masa asusu da ake kira wallet a shafukan da ake harkar. Haka suma sauran kuɗaɗen Intanet kamar su Ethereum, Litecoin da sauransu....



Wannan a takaice Kenan a Halin yanxu shawara idan kana son Fara harkar CRYPTOCURRENCY to kasamu malami Wanda yasan harkar ya koya maka soar


Dan ina tambbatar muku dacewa koda baka Shiga yanxu ba toh nan gaba insha'Allah sai kashiga, Duniya zata samu  wani Revalution Wanda dole sae Ka Shiga andama dakae.


Shawarace Dan karkazo kazama kwararet😂😂😂



Bin Ousmanee News Live

 

Post a Comment

0 Comments